Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

yarjejeniyar Nukiliya Da Iran: Ba Amurka Ce 'Yarsandan Duniya Ba-Faransa.


Shugaban Faransa Eammanuel Macron da ministar harkokin wajen EU Federica Mogherini.
Shugaban Faransa Eammanuel Macron da ministar harkokin wajen EU Federica Mogherini.

A makon gobe ake sa ran ministocin harkokin wajen Britaniya, da Faransa, da Jamus, za su gana da takwaran aikin su na Iran a Brussells.

Ana sa ran ministar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federicka Mogherini, zata jagoranci taro da ministocin harkokin wajen Britaniya, da Faransa, da Jamus a Brussels ranar talata mai zuwa domin su tattauna kan makomar yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran kan shirin Nukiliyarta, ganin cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya janye Washington daga yarjejeniyar.

Ofishin ministar ta fada cikin wata sanarwa da ta fitar jiya jumma'a cewa, ministan harkokin wajen Iran Javad Zariff, shima zai gana da minisotcin harkokin wajen kasashen uku tareda Mogherinin.

Haka nan shugabar Jamus Angela Merkel, ta zanta da shugaban Rasha Vladimir Putin kan janyewar ta Amurka. Merkel ta ce janyewar Amurkan zata yi zagon kasa ga yarjejeniyar kasa da kasan, duk da haka ofisoshin shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin ci gaba da mutunta yarjejeniyar.

Yayinda ministan harkokin wajen Faransa yake kira ga turai ta kare diyaucin tattalin arzikinta saboda Amurka ba itace 'yar sandan duniya ta fuskar tattalin arziki ba.

A gefe daya kuma Rasha tace ita da wasu kasashe suna tattaunawa na nkulla yarjejeniyar cinikayya da Iran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG