Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TURKEY: Wasu Sun Kai Hare-haren da Suka Hallaka Mutane a Istanbul


Wyrin da aka kai hre-hare abirnin Itanbul babban birnin kasar Turkiya

Yau Litinin kasar Turkiya ta fuskanci wasu jerin hare-hare da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Wasu jerin hare-hare- da aka kai akan ‘yan sanda da Sojoji a yau Litinin ya yi sandaiyar mutuwar mutane da dama a Turkiya, yayin da aka kai wani hari na daban a kan ofishin Jakadancin Amurka a Istanbul babban birnin kasar.

Babu dai wanda ya ji koda rauni a lokacin da wasu mutane biyu suka kai harin na ofishin jakadancin Amurkan.

Sai dai maharan sun samu sun kubuce, bayan da ‘yan sanda suka mayar musu da martini.

Amma daga baya ‘yan sanda sun ce sun cafke daya daga cikin maharan wacce ta kasance mace.

Hukumomin sun ce a da matar mamba ce a jam’iyyar People’s Liberation Party me rajin samar da sauyi.

Kasar ta Turkiya da Amurka da kungiyar tarayyar Turai, na yiwa wannan kungiyar kallon ‘yan ta’adda, wacce ta sha kai hare-hare, ciki har da wanda ta kai ofishin jakadancin Amurka da ke Ankara a shekarar 2013.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG