Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TURKIYA; Ta Soma Kai Hari Kan Kungiyar ISIS a Siriya


Motar sojoji ta datse kan iyakar Turkiya da Siriya bayan hare-hare

Kasar Turkiyya tace takai hare-hare ta sama kan ISIS a Siriya, a wani yunkuri na ganin an dakile kungiyar ta masu tsatstsauran ra’ayi.

Jirage uku kirar F-16 ne suka tashi daga birnin Diyarbakir dake kudu maso gabashin Turkiyya a safiyar yau Juma’a, sun kuma auna mayakan dake tsallaken iyakar Turkiyyar a lardin Kilis, a cewar ofishin Firayim Minista.

Wata sanarwa tace jiragen sama sun jefa boma-bomai hudu a wasu hedikwatar ISIS har biyu, da wani guri da ‘yan kungiyar ke haduwa kafin jiragen su koma sansanin su lafiya.

A lokacin da Firayim Minista Dovutoglu yake magana da taron manema labarai, yayi rantsuwar gwamnatinsa ba zata kawar da kai ba ga harin da ake kaiwa Turkiyya.

Mr. Davutoglu ya cigaba da cewa “daga safiyar yau, sojojin Turkiyya zasu yi amfani da umarni da aka basu daga gwamnati, zasu kumaauna duk inda a kace musu ba tare da samun tangarda ba, har sai an ga bayan su.”

Wannan dai shine karon farko da Turkiyya tayi amfani da jiragen sama wajen auna mayakan ISIS a Siriya.

Haka ma yau Juma’a, Jami’an Turkiyya sunce sun kame mutane 251 a lokacin wani samame da ‘yan sanda suk kai kan ‘yan kungiyar ISIS da mayakansu dake wasu wurare a fadin kasar.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG