Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TURKIYA: Amurka ta Bukaci Kasar ta Kara Kaimi a Yaki da ISIS


Ashton Carter Sakataren Tsaron Amurka

Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter, yayi kira ga kasar Turkiyya ta kara himma a yaki da kungiyar ISIS kuma ta kare kan iyakokinta.

Sakatare Carter yace Turkiyya ta amince bisa ka'ida ta shiga sahun rundunar taron dangi ta mayakan sama da Amurka take yiwa jagoranci, a fafatawa da mayakan ISIS, sai dai yace wannan wani bangare ne cikin matakai da suka kamata Turkiyya ta dauka.

Sakataren tsaron na Amurka ya kara da cewa a zaman makwabciya ga kasashen da ake rikici watau Syria da Iraqi, akwai bukatar Turkiyya ta kara kiyaye kan iyakokinta fiye da abunda ta yibara.

Sakataren tsaron yace mayakan ISIS da kayan aiki suna ketarowa daga Turkiyya su shiga Syria da Iraqi ba tare da wata matsala ba.

Mr. Carter yace ba ya tunanin kamar Turkiyya "tana jan kafa", amma yace da ya kamata ace warhaka duka kasar ta shiga sahun kasashe da suke kai farmaki da jiragen yaki kan ISIS.

Yace yanzu shekara daya da fara kai farmaki kan ISIL, Turkiyya tana kokari sosai yanzu bisa dukkan alamu, ciki harda kyale Amurka tayi amfani da wani sansanin sojinta na sama. "hakan yana da muhimmanci" amma akwai bukatar ta kara.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG