Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiya da Rasha Sun Shiga Takunsaka Kan Kakkabo Jirgin Yakin Rashan


Samfarin jirgin yakin Rasha da Turkiya ta kakkabo
Samfarin jirgin yakin Rasha da Turkiya ta kakkabo

An samu zaman tankiya tsakanin Turkiya da Rasha saboda Turkiya ta kakkabo jirgin yakin Rasha wanda tace ya keta mata sararin samaniyar kasarta, zargin da Rasha ta musanta tare da alakanta abun da Turkiya ta yi da ta'adanci.

Sa'o'i kadan bayan da Turkiya ta kakkabo wani jirgin yakin saman Rasha akan iyakar kasar da Syria shugaban Amurka Barack Obama da takwaransa na kasar ta Turkiya Recep Tayyip Erdogan sun amince akwai bukatar a rage zaman tankiya domin a kiyaye tashin hankali.

Fadar White House ta shugaban Amurka a wata sanarwa da ta fitar jiya Talata tace shugabannin biyu sun tattauna ta wayar tarho inda suka sake jaddada aniyarsu ta ganin an kafa gwamnatin wucin gadi da zummar kawo zaman lafiya a kasar Syria. Sun kuma nemi goyon bayan kasa da kasa domin murkushe kungiyar ISIS. Sanarwar ta goyi bayan 'yancin Turkiya ta kare sararin samaniyar kasarta.

Yayinda yake jawabi lokacin ziyarar shugaban Faransa Francois Hollande zuwa Fadar ta White House Shugaban Amurka Barack Obama yace hukumomin Amurka suna cigaba da tara bayanai akan kakkabo jirgin Rasha da Turkiya ta yi. Amma ya kara da cewa jiragen yakin Rasha suna auna hare-harensu ne akan 'yan tawayen Syria masu sassaucin ra'ayi da suke da sansaninsu kusa da iyaka da Turkiya.

Shugaba Obama ya kara da cewa lamarin da ya faru nuni ne cewa a hanzarta a kawo karshen rikicin Syria ta hanyar diflomasiya.

A nashi martani da ya mayar daban Shugaban Rasha Vladimir Putin wanda gwamnatinsa ta hakikice cewa jirgin yakin kasar bai taba keta kasar Turkiya ba , ya zargi gwamnatin kasar Turkiyar da yiwa Rasha yankan baya da kakkabao jirgin lamarin da ya alakanta da ta'adanci

XS
SM
MD
LG