Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiya da Tarayyar Turai Sun Amince da Shirin Magance Kwararar Bakin Haure


Sansanin bakin haure a Turkiya
Sansanin bakin haure a Turkiya

Kasar Turkiyya da Kungiyar Tarayyar Kasashen Turai, sun amince da wani shiri da zai lakume biliyoyin daloli, wanda zai magance matsalar kwararar bakin haure da ya addabe su, yayin da yake-yake a sassan duniya ke tilasawa mutane ficewa daga gidajensu.

A wani taron koli da aka yi a Brussels, babban birnin Belgium, kungiyar ta tarayyar turai ta samarwa da Turkiyya da agajin kudi na dala biliyan 3.2, domin ta lura da miliyoyin ‘yan gudun hijrar da ke zaune a kasar ta Turkiyya.

Babbar tawagar ‘yan gudun hijra daga Syria wadanda suka isa nahiyar Turai a wannan shekara sun ratsa ta Turkiyya, yayin da su ke kan hanyarsu ta zuwa Girka da Bulgaria.

Shugaban kwamitin kungiyar ta tarayyar turai Donald Tusk, ya fada a taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gabatar tare da Firai ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu da shugaban kwamitin zartaswar kungiyar kasashen turai Jean-Claude Juncker cewa, matsayar da aka cimma, ta tsara yadda za a samar da daidaito a iyakokin kasashen nahiyar.

Tusk ya kara da cewa za a kara assasa batun yunkurin da Turkiyyan ke yi na samun gindin zama a kungiyar kasashen turan.

A shekarar 1997 aka ayyana Turkiyya a matsayin kasar da ta cancanci ta shiga kungiyar, inda tuni ta fara shirye-shiryen samun gurbi na dindindin a shekarar 2005 a hukumance.

XS
SM
MD
LG