Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Na Neman Izinin Bincikar Ofishin Jakadancin Saudiyya


Turkiya ta nemi izinin a jiya Litinin daga Saudi Arabia ta binciki ofishin jakadancin Saudiyar a Istanbul, domin gano dalilin bacewar wani dan jaridar Saudi Arabia da jami’an Turkiya suka ce an kashe shi a cikin ofishin jakadancin.

Yarimar masarautar Saudiya Mohammed bin Salman ya fada a makon da ya gabata cewa a shirye Riyadh take ta tarbi gwamnatin Turkiya kuma su binciki ofishin jakadancinta, saboda babu wani abu da take boyewa, game da bacewar dan jaridar nan mai shekaru 59 da haihuwa Jamal Khashoogi.

Sai dai ba a gano nan da nan ko jami’an Turkiya sun samu izinin shiga ofishin jakadancin Saudiyar bayan sun nemi izinin yin haka a jiya Litinin. Jami’an Saudiya sun ce zargi da masu binciken Turkiya suke yin a kashe Khashoogi bashi da wani makama.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan yace tilas ne jami’an Sadui Arabia su fito da shaidar dake nuna Khashoogi ya bar cikin ginin ofishin jakadancinsu bayan ya isa ofishin a ranar Talatar makon da ya gabata domin karbar takardun daurin aurensa da yake shirin yi. Matar da yake niyar aurenta Hatice Cengiz da take jirarsa a wajen ofishin, tace bai fito daga cikin ginin ba.

Shugaba Erdogan ya fada yayain da yake ziyara a babban birnin kasar Hungary Budapest, cewa lallai ne zamu samu sakamakon wannan bincike cikin gaggawa. Yace jami’an ofishin jakadancin ba zasu iya kare kanu da maganar baki kadai ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG