Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta Yi Asarar Sojointa 7 A Siriya


Firaministan Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan
Firaministan Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan

Kasar Turkiyya ta amsa cewa ita ma ta dan dandana kudarta a yakin da ta kaddamar kan Kurdawan Siriya, wadanda ta ce su na hada kai da 'yan'uwansu da ke Turkiyya, wajen yin mata zagon kasa. Sojojinta akalla 7 ne su ka mutu jiya a wannan fadan.

Rundunar Sojin Turkiyya ta ce ta yi asara mafi muni ta rayukan sojojinta a rana guda, a farmakin da ta ke kai wa kan ‘yan bindiga a arewacin Siriya.

Sojojinta akalla 7 su ka mutu jiya Asabar.

Biyar daga cikinsu sun mutu ne a yankin Afrin, lokacin da aka kai hari kan tankar yakin da su ke ciki.

Biyu kuma sun mutu ne tun da farko a jiya din - daya daura da inda aka kai hari kan tankar yakin, dayan kuma daura da kan iyakar Siriya da Turkiyya.
A martanin da ta mayar, Turkiyya ta ce ta jiragen yakinta sun kai hari kan wasu wurare na Turkiyya da ke yankin da aka kai hari kan tankar yakin.
Tun a karshen watan jiya ne Turkiyya ta fara kaddamar da farmaki kan dakarun Kurdawan YPG da ke Siriya, wadanda Turkiyya ke daukawa a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda masu alaka da Kungiyar awaren Kurdawa da ke Turkiyya. Zuwa yanzu dai Turkiyya ta rasa sojoji 14 a wannan fadan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG