Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tutu Yace A Gurfanar Da Bush Da Blair A Gaban Kotu


Babban fada, Archbishop Desmond Tutu, tsohon shugaban darikar Anglican na Afirka ta Kudu

Babban fada Archbishop Desmond Tutu yace George W. Bush da Tony Blair sun kafa hujjar karya don kai farmaki a kan kasar Iraqi a shekarar 2003

Babban fada Archbishop Desmond Tutu na Afirka ta Kudu yace tsohon shugaban Amurka, George W. Bush, da tsohon firayim ministan Britaniya, Tony Blair, sun dauki matakan da suka nuna cewa su 'yan cin zali ko fin karfi ne a shawarar da suka yanke ta kai farmaki kan kasar Iraqi a shekarar 2003, saboda haka ya kamata a gurfanar da su a gaban shari'a domin su amsa abubuwan da suka yi.

A cikin wata caccaka mai zafin gaske da yayi a kan mutanen biyu cikin jaridar Observer ta kasar Britaniya, Archbishop Tutu ya rubuta cewa, “Bush da Blair sun tura mu ga bakin ramin kura inda muka tsinci kanmu a yanzu, inda muke kallon batun kasashen Sham da Iran a gabanmu.”

Archbishop Tutu ya ce an kafa hujjar kai farmaki kan kasar Iraqi ne bisa “karyar cewa Iraqi ta mallaki makaman kare dangi.” Yace wannan shawara ta gurgunta ta kuma raba kawunan duniya fiye da kowane lamari a tarihin duniya.

Jagoran akidar zaman lafiyar dan Afirka ta Kudu, kuma tsohon babban limamin Kiristoci mabiya darikar Anglican na kasar, yace ana nuna bambanci wajen auna kimar shugabannin kasashen yammaci idan an kwatanta da na Afirka. Yace irin hasarar rayukan da aka yi a lokacin yakin Iraqi da kuma bayansa ya kai mizanin da ya kamata a ce an gurfanar da Mr. Bush da Mr. Blair a gaban kotun duniya.

Archbishop Tutu yace, "da a ce duniya da gaskiya, to ya kamata a ce mutanen da suka haddasa irin wannan bakar wahala da mace-mace sun bi sahun shugabannin Afirka da na Asiya wadanda aka kai su birnin Hague aka gurfanar da su gaban shari’a (a kotun duniya).”

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG