Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UEFA: Manchester City Ta Kai Wasan Karshe Bayan Doke PSG Da Ci 2-0


Lokacin da Mahrez ya ci kwallo a wasansu da Burnley

Yanzu City za ta ja gefe ta jira wanda za ta kara da shi a wasan karshe tsakanin Chelsea da Real Madrid.

Manchester City ta samu nasarar kai wa ga wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar turai na UEFA league da ake yi.

Hakan na faruwa ne bayan da ta doke Paris Saint Germain da ci 2-0 a wasansu na zagaye na biyu a gidan City.

Riyad Mahrez ne ya zura kwallayen biyu, ta farko a minti na 11 ta biyu kuma a minti na 63.

A wasan farko, City ta bi PSG har Paris ta make ta da ci 2-1. Hakan ya zama City ta lashe wasannin da ci 4-1 kenan a jimullance.

An kori Angel de Maria da jan kati a wasan.

Yanzu City za ta ja gefe ta jira wanda za ta kara da shi a wasan da za a kara tsakanin Chelsea da Real Madrid.

Chelsea da Madrid sun tashi da c- 1-1 a wasan farko a Estadio Alfredo Di Stéfano.

Yanzu za su hadu a Stamford Bridge a Ingila a ranar Laraba.

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG