Bayan da aka kammala wasanni a zagayen Quarter-final a neman lashe kofin zakarun turai, yanzu kulob hudu sun kai zagayen semi-final.
A zagayen farko, Real Madrid za ta kara da Chelsea a ranar 27 ga watan Afrilu, sai kuma su sake karawa a zagaye na biyu a ranar 5 ga watan Mayun.
Sannan PSG za ta kara da Manchester City a ranar 28 ga watan Afrilu a zagayen farko sai kuma sake haduwa a ranar 4 ga watan Mayu.
Tuni dai an yi waje rod da Liverpool da Borussia Dortmund a zagayen quarter-final da aka kammala a zagaye na biyu a ranar Laraba.
Yanzu masoya kwallon kafa, musamman a shafukan sada zumunta, na tafka muhawara kan kungiyoyin da za su kai wasan karshe a wannan gasa.