Accessibility links

A Kenya Uhuru Kenyatta Ne Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar.

  • Aliyu Imam

Shugaban Kenya mai jiran gado, Uhuru kenyatta yake gaida magoya bayansa, bayanda hukumar zabe ta ayyana shi a marsayin wanda ya lashe zaben kasar.
A hukumance hukumar zabe a Kenya ta ayyana Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na farko da aka yi tun shekara ta 2007.

Shugaban hukumar zaben kasar Issack Hassan ya fada yau Asabar cewa Mr. Kenyatta ya sami kashi 50 da digo bakwai, da wannan sakamakon da kiris ya kaucewa a gudanar da zaben fidda gwani.

Frayin Minista Ra’ila Odinga ne yazo na biyu a zaben kasar da aka gudanar ranar litinin, da kuri’u kadan ya dara kashi 43 cikin dari na kuri’u da aka kada. Mr. Odinga ya yi magana kan irin magudi ko kaucewa tsarin zaben da aka yi, ya fadi haka ne a jawabi da yayi yau Asabar, yace bashi da niyyar amincewa da sakamakon zaben.

Ahalinda ake ciki kuma kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ta dage jinkirta sauraron karar da aka shigar kan mataimakin Mr. Kenyatta William Rutto, daga 10 ga watan Afrilu zuwa 28 ga watan Mayu.

Mr. Rutto da Uhuru Kenyatta duk suna fuskantar zargin kitsa tarzomar kabilanci da ta biyo bayan zaben 2007 zuwa 2008. Ranar Alhamis kotun ta dage sauraron tuhumar da ake yiwa Mr. Kenyatta daga Adfrilu zuwa watan Yuli.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG