Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine Ta Shiga Tsaka Mai Wuya Daga Hare-Haren Rasha Na Makami Mai Lizzami 122


Russia Ukraine War
Russia Ukraine War

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya fada a jiya juma’a cewa Ukraine tana yakin ceton rai, bayan da Rasha ta kai gagaruman farmaki a fadin Ukraine.

A jawabinsa na duk wuni, Zelenskyy ya ce lugudan wutar ya hada da makamai masu linzami da jirage mara matuka 160, ya kwatanta hare haren da mummunar fatattaka ta cin mutuncin dan Adam.

Zelenskyy ya ce ana gudanar da ayyukan ceto a garuruwan da harin na Rasha ya shafa.

Zamu dau fansa a kan duk harin ‘yan ta’addan Rasha. Ta’addanci baya galaba a kan mutane, in ji Zelenskyy.

Sai dai jami’ai a Moscow sun fada a yau Asabar cewa rundunar tsaron sararin saman Rasha ta kakkabo gomman jirage mara matuka da Ukraine ta harba a Moscow, a yankunan Bryansk, Oryol da Kursk.

A jiya Jumma’a, kwamitin sulhu na MDD ya yi wani taro a kan munanan hare hare ta sama da Rasha ta kai kan Ukraine, da bata taba yin irin shi ba tun fara yakin a cikin watan Fabrairun 2022, inda ta kaddamar da makamai masu lizzami 122 da gomman jirage mara matuka a cewar jami’an Ukraine.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG