Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya-Shirin Yaki da Talauci


Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon, ya yi kira ga Shugabannin kasashe da su kara azama a kudurinsu na rage talauci, da yunwa da cututtuka

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon, ya yi kira ga Shugabannin kasashe da su kara azama a kudurinsu na rage talauci, da yunwa da cututtuka a fadin duniyan nan a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Mr. Ban ya bude taron kwanaki uku jiya Litini a birnin New York, wanda ya gama Shugabanni da Firayim Ministocin kasashe 140, don yin bitar maradun karni da aka kaddamar a 2000.

Wannan shirin dai na da manufar cimma nasara a bangarori 8, ciki har da batun shawo kan matsanaciyar yunwa, da rage yawan mutuwar yara kanana, da inganta lafiyar uwaye da kuma wanzar da ilimin firamare.

Mr. Ban ya lura cewa an sami cigaba wajen neman cimma wadannan bukatun, to amman ya ce har yanzu da jan aiki. Ya ce muradun na tayar komada sosai, ya kuma yi kira ga Shugabanni da su “cika alkawuransu.”

Da ya ke jawabi ga taron jiya Litini, shi ma Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, ya yi kira ga Shugabannin kasashen da su nemi hanyoyi cika alkawuransu. Ya ce Faransa za ta kara gudunmowarta ga asusun yaki da cutar AIDS da tarin fuka da zazzabin cizon sauro na Majalisar Dinkin Duniya da kashi 20% a shekaru 3 masu zuwa.

XS
SM
MD
LG