Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNHCR Na Bukatar $157m Domin Kulawa Da 'Yan Gudun Hijirar Kasashen Tafkin Chadi


Taron Jakadun UNHCR dake kasashen yankin tafkin Chadi
Taron Jakadun UNHCR dake kasashen yankin tafkin Chadi

A taron jakadun UNHCR da aka yi a Yamai aka fayyace tsarukan ayyukan da za'a yi bana tare da adadin kudin da ake bukata domin gudanar da ayyukan

A karshen taron jakadun UNHCR dake kasashen yankin tafkin Chadi da aka gudanar a birnin Yamai a kasar Nijar aka fayyace tsarin ayyukan da za'a gudanar a bana, shekarar 2018.

Shirin zai shafi sama da mutane 250 da rikicin Boko Haram ya daidaita. Cikinsu akwai 'yan gudun hijiran Najeriya sama da dubu 208. Matsalr ta shafi masu masaukin baki su sama da dubu 75 a kasashen Nijar, Chadi da Kamaru.

Mataimakiyar kwamishanar UNHCR ta ce zasu yi anfani da kudaden a fannonin da suka hada da ci gaban ayyukan rajistan 'yan gudun hijira a Diffa, yankin da ya fi koina samun bakuncin 'yan gudun hijiran Najeriya.

Za'a yi anfani da kudin wurin samar da abinci ga al'umma bisa ga yin la'akari da cewa a watan Satumbar 2017 an gano mutane miliyan bakwai da rabi ne suke cikin karancin abinci a Nijar. Kana za'a mayar da hankali akan sha'anin ilimi saboda bincike ya nuna cewa kashi 85 cikin 100 na 'ya'yan mutanen da suka yi hijira a yankin basa zuwa makaranta.

Kazalika za'a dauki matakan samar da cimaka mai gina jiki ga yara kanana da kuma inganta kiwon lafiya.

Hukumar UNHCR na kokarin shawo matsalar rajistan yaran da aka haifesu a sansanonin 'yan gudun hijira ta hanyar wayar da kawunan jama'a musamman a kasar Kamaru inda makiyaya ke ketarawa zuwa Najeriya domin neman ciyawar dabbobi, inji wakilin 'yan gudun hijira a kasar ta Kamaru.

Jakadan UNHCR a kasar Chadi ya bayyana cewa ci gaban tabarbarewar tsaro a kewayen tafkin Chadi na kawo cikas ga jami'an agaji wajen isar da doki ga 'yan gudun hijira a kasar ta Chadi.

Baya ga 'yan gudun hijiran Najeriya, Nijar na samun bakuncin 'yan gudun hijiran kasar Mali wadanda tuni wasu cikinsu suka fara gudanar da sana'o'i, lamarin da ya sa ana ganin wasunsu ba zasu koma inda suka fito ba duk da ikirarin da UNHCR tayi na cewa mayar da su magana ce ta dan lokaci.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00


.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG