Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UNICEF: Yara Miliyan Hudu Ne Basa Makaranta A Afghanistan


Hukumar Majalisar Dinkin Duniya dake kula asusun rayar da yara
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya dake kula asusun rayar da yara

Hukumar dake kare muradun yara ta Majalisar Dinkin Duniya ,UNICEF adadin yaran da suka isa zuwa makaranta amma basa zuwa a Afghanistan ya dara miliyan hudu

Hukumar da ke kare muradun yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ta ce, kusan rabin adadin yaran da suka isa zuwa makaranta a Afghanistan, wato kusan miliyan hudu kenan, ba sa zuwa makaranta saboda rikice-rikicen da kasar ke fama da su.

Sakamakon wannan bincike, wanda aka fitar da shi a wani sabon rahoto, na nuni da irin koma-bayan da kasar ke ci gaba da fuskanta.

Rabon da aka ga wannan yawan adadi na yaran da suka bas a zuwa makaranta, tun a shekarar 2002, wato jim kadan bayan da aka kawar da kungiyar Taliban.

Yayin wata ganawa da ta yi da manema labarai, Darektar UNICEF, Henrietta Fore, ta ce, “idan yara mata da maza suka fita a makaranta, yana da matukar wahala su koma.”

Nazarin da aka yi, ya nuna cewa, al’adar aurar da kananan yara mata, shi ne dalili na biyu a jerin dalilan da ke sa mata suke fita a makarantu.

Sai dai wani labari mai faranta rai da binciken ya gano, shi ne, adadin masu fita a makarantar ya kan ragu, idan har suka riga suka fara makarantar, inda kashi 85 na adadin yaran da suka fara firaimare da kuma sama da kashi 90 na wadanda suka fara sakandare, sukan kammala karatunsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG