Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa A Jihohi 37 Suna Zaben Gwamnoni Da Ake Ganin kamar 'Yan Republican ne Zasu Samu Rinjaye


A wan nan hoto mai kada kuri'a ne yazo wurin zabe,a zaben 'yan majalisar Amurka.

Ahalin yanzu Jam'iyyar ta Republicans tana da Gwamnoni 23,kuma a karshen wan nan zabe na karshen wa'adin wakilan majalisar dokokin Amurka ana jin zata kama karin wasu jihohi shida.

Talata masu zabe a jihohin Amurka 37 suke kada kuri’ar zaben gwamnoni da ake ganin kamar ‘yan takarar jam’iyyar Republican ne suke kan gaba.Jam’iyyar Republican da take da gwamnoni 23,ana ji zata kara kama wasu shida.

A kuri’ar ta yau Talata ana zabe a wasu manyan jihohi masu dumbin jama’a, da jam’iyu suke kwadayi,ciki har da California,Florida,Ohio, Pennsylvania,da kuma Texas.

Bisa tarihi jihohi suna taimakawa ‘yan takarar shugaban kasa samun nasarar shiga fadar White House,hakan ya ta’allaka ne kan jam’iyyar da take mulkin jiha.

Sabbin gwamnonin ne hakkin shata sabbin mazabu ya rataya a wuyansu,bisa sakamkon kidayar jama’a ta 2010.

Wata matsla da jihohi suke fuskanta har da Karin rashin aikin yi,wacce ta fi addabar jihar Ohio. Saura sun hada da gibin a kasafin kudade,wacce ta fi shafar jihar California, fiye das aura.

XS
SM
MD
LG