Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Jam'iyyar Republican Sun Sha Alwashin Taka Wa Gwamnatin Tarayyar Amurka Birki


Ginin majalisar dokokin Amurka.

Kakakin Majalisar Wakilan Amurka mai jiran gado John Boehner ne ya bayyana haka ga manema labarai,cewa ganin yanzu ita jam'iyyar Republican ce take da rinjaye a majalisar wakilai,da karin kujeru a majalisar dattijai

Shugabannin jam’iyyar Republican sun ci alwashin rage karfin fada ajin da Gwamnatin tarayyar Amurka keda shi tunda yanzu Republican ce keda rinjaye a majalisar wakilan Amurka tare da samun Karin kujeru a majalisar dattawa.

Dan majalisa kuma wanda zai haye kujerar kakakin majalisa John Boehner, ya shaidawa taron manema labarai laraba, cewa rinjayen da Republican ta samu a majalisar wakilai zai karfafa muryar Amerkawa ne a majalisa, kuma jam’iyyar Republican zata ci gaba da karfafa kokarinta wajen rage karfin Gwamnatin tarayya.

A watan Janairu mai zuwa ne sabuwar majalisar dokokin Amurka zata fara zamanta.

XS
SM
MD
LG