Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

US Was Ready to Accept Palestinian Refugees-Olmert


Tsohon Firayim Ministan Isira’ila,ya ce Amurka ta bayyana niyyar rungumar yan gudun hijirar Falasdinawa 100,000 a matsayin wani sharadi na shirin zaman lafiya na 2008

Tsohon Firayim Ministan Isira’ila, Ehud Olmert, ya ce Amurka ta bayyana niyyarta ta rungumar yan gudun hijirar Falasdinawa 100,000 a matsayin wani sharadi na shirin zaman lafiya na 2008. Idan har aka yi nasara a tattaunawa ta yanzu, a cewar Mr. Olmert, zai yi zaton za a cimma yarjajjeniya makamanciyar shawarar da ta cije shekaru biyu da su ka gabata.

Da ya ke Magana jiya Lahadi a birnin Tel Aviv, Mr. Olmert ya ce tsohon Shugaban Amurka George W. Bush ya ba shi tabbacin cewa Amurka za ta karbi yan gudun hijira 100,000 ta kuma ba su izinin zama yan kasa a matsayin daya daga cikin matakan daidaitawa ta dindindin tsakanin Isira’ila da Hukumar Falasdinawa.

Mr. Olmert ya ce shawararsa ta 2008 ta cimma zaman lafiya na da niyyar la’akari da wahalar dubban Falasdinawan da su ka rasa gidajensu bayan da aka kaddamar da kasar Isira’la sama da shekaru 60 da su ka gabata. Tsohon Firayim Ministan Isira’ila din ya ce Isira’ila ta yi niyyar amincewa ta karbi wani karamin rukuni na Falasdinwa—watakila kasa da 20,000---bisa dalili na jinkai.

Ran Lahadi da safe, Ministan Harkokin Wajen Isira’ila Avigdor Lieberman ya bayar da shawarar cewa Isira’ila ta sake fasalin taswirar kasarta ta yadda wasu Falasdinawa za su kasance a karkashin ikon Falasdinu, a sa’ilinda ita kuma za ta cigaba da mallakar matsugunan Yahudawan da ke yamma da kogin Jordan.

Lieberman ya ce bai kamata tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isira’ila da Falasdinawa ta ta’allaka kan sallamar da kasa don samun zaman lafiya ba wanda ke nufin kawo karshen mamayar yankunan Falasdinawa da Isira’ila ke yi, sai dai ko ya zama sallamar da kasa da jama’arta don samun zaman lafiya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG