Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uwargidan Shugaban Amurka Malania Trump Ta Isa Malawi


Uwargidan Shugaban Amurka Melania Trump A Malawi

Yanzu haka Melania Trump, matar shugaban Amurka, tana kasar Malawi a yau Alhamis, kasa ta biyu da take ziyara a rangadin da take na wasu kasashen Afrika.

Da saukarta birnin Lilongwe, Melania ta je ta ziyarci wata karamar makarantar firamare wacce ke da dalibbai kamar 8,000 amma malamai 75 kacal. Ta ma zauna ta kalli yaran suna daukan darasin koyon turancin Ingilishi, kuma daga bisani ta zanta da malaman makarantar.

Matar shugaban na Amurka tazo da tsarabar da fadar White House ta baiwa ‘yan makarantar, wacce ta hada da jakuna, alli da kuma kwallayen kafa.

Haka kuma ance ita ma Hukumar raya Kasashe ta Amurka, USAID, tana shirin bada kyautar tarin littafai ga makarantar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG