Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uwargidan shugaban Najeriya ta shawarci iyaye su bari a yiwa ‘ya’yansu rigakafi


Wata jaririya ana diga mata maganin rigakafi

Uwargidan shugaban kasar Najeriya Patience Jonathan ta shawarci iyaye su tabbata an yiwa ‘ya’yansu allurar rigakafi

Uwargidan shugaban kasar Najeriya Patience Jonathan ta shawarci iyaye su tabbata an yiwa ‘ya’yansu allurar rigakafi, an kuma basu sinadarin Vitamin A.

Uwargidan shugaban kasar ta yi wannan jiran ne yayin bukin makon mata masu juna biyu da kanannan yara na kasa.

A cikin jawabinta ta bakin uwargidan shugaban majalisar dattijai Helen Mark tace, “ina karfafa dukan iyaye da wadanda hakin kula da kananan yara ya rataya a wuyansu, su tabbata sun kai kananan yaran da shekarunsu suka gaza biyar zuwa dakin magani domin yi masu rigakafi da kuma basu sinadarin Vitamin A, da maganin tsutsar ciki.

Uwargidan shugaban kasar tace ba za a lamunci halin da ake ciki a Najeriya ba inda kimanin kananan yara 157 daga cikin 1,000 suke rasa rayukansu kafin su cika shekaru biyar, yayinda mace daya cikin goma sha uku take rasa ranta wajen haihuwa.

Mrs Jonathan ta kuma kalulabanci ma’aikatan jinya su kara kwazo a bakin aiki su kuma tabbatar kowanne karamin yaro ya sami magani.

Bincike na nuni da cewa, kimanin jarirai 1400 da kuma wani Karin kananan yara 970 suke mutuwa kowacce rana. Najeriya na daya daga cikin kasashen da kananan yara suka fi mutuwa a duniya sakamakon rashin kula da lafiyarsu da kuma kamuwa da cututukan da za a iya maganinsu.

XS
SM
MD
LG