Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamhuriyar Nijer Uwar Jam’iyar PNDS TARAYYA Wai Mulki ta Bada Sanarwar Korar Wani Babban Jigonta ALHAJI IBRAHIM YACOUBA.


Shugaba Nijer Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar nijer uwar jam’iyar PNDS TARAYYA wai mulki ta bada sanarwar korar wani babban jigonta ALHAJI IBRAHIM YAKUBA mai rike da mukamin matemakin darektan fadar shugaban kasa bisa zarginsa da laifin bijirewa umurnin jam’iya.

Wakilin muryar amurka a yamai sule mumuni barma ya aiko mana rahoto akai.

Wannan sabon rikici ya samo asali daga wani shirin sabinta rassan jam’iyar ta pnds tarayya a jihar dogon dutsi dake yankin DOSSO da ya ci tura a ranar lahadin da ta gabata wanda har sai ‘yan sanda suka shiga tsakani sakamakon sabanin da aka samu tsakanin magoya bayan IBRAHIM YAKUBA da na matemakin shugaban jam’iyar na kasa baki daya PIERRE FOUMAKOYE GADO.

dan majalisar dokokin kasa zakari umaru memba a kwamitin kolin pnds tarayya ya bayyana mana yanda abubuwa suka wakana .

jam’iyar ta pnds tarayya tace bayan nazari akan abinda ka iya biyo baya ta yankae shawarar korar ibrahim yakuba daga sahun ‘yayanta kuma har ma tayi kashedi a gareshi.

Na bugawa matemakin shugaban na fadar shugaban kasa waya domin ya maida martani amma bai daga waya ba na kuma aika masa sakon sms har i zuwa lokacin da nake aiko da wannan rahoto bai bani amsa ba sai dai da yake tsokaci a shafin sada zumunta na face book ALHAJI IBRAHIM YAKUBA ya bayyana cewa ya yi na’am da matakin na uwar jam’iya.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

XS
SM
MD
LG