Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wa Ya Karkatar Da Naira 2.67B Na Ciyar Da ‘Yan Makaranta?


shugaba Muhammadu Buhari
shugaba Muhammadu Buhari

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin jami’an gwamnatin Najeriya ICPC ta fayyace bayanin da ta yi kan batun karkatar da kudin ciyar da ‘yan makaranta da tace an yi a rahoton da shugaban hukumar ya gabatar a fadar shugaban kasa.

A cikin sanarwar da hukumar ICPC ta bayar ranar Litinin ta hannun kakakinta Azuka Ogugua, hukumar ta bayyana cewa, ba a fahimci bayanin da shugaban hukumar Farfesa Bolaji Owanoye ya gabatar ba ne, aka dauka yana magana ne a kan shirin da ake aiwatarwa karkashin Ministar ayyukan jinkai da samar da ababan jin dadin rayuwa Sadiya Farouq .

Kakakin hukumar ta bayyana cewa shirin ciyar da daliban makarantun sakandare na gwamnatin tarayya da ke gida a halin yanzu sabili da rufe makarantun da aka yi da nufin dakile yaduwar cutar Coronavirus ake magana a kai, amma ba shirin ciyar da yaran makarantar firamare da abincin da ake nomawa a garuruwansu ba da ke karkashin ma’aikatar ayyuka jinkai da inganta rayuwa.

an-kai-karar-shugaba-buhari-a-babbar-kotun-tarayya

an-fara-bincike-kan-kudaden-covid-19-a-najeriya

hukumar-icpc-ta-kai-ziyara-jihar-kebbi-don-bibiyar-wasu-ayyuka

A cikin rahoton da Shugaban Hukumar ICPC Farfesa Bolaji Owasanoye ya bayar a fadar shugaban kasa ranar Litinin da ta gabata, ya bayyana cewa, hukumar ta gano Naira biliyan 2.67 da aka ware domin ciyar da daliban makarantun sakandare na gwamnatin tarayyar a asusun ajiyar wadansu mutane, da ta ce tana kan gudanar da bincike.

Sadiya Umar Farouq
Sadiya Umar Farouq

Kwana guda bayan gabatar da rahoton, Ministar ayyukan jinkan ta fito da sanarwa ta musanta rahotannin da ake yayatawa cewa ta karkatar da Naira 2.7b kudin ciyar da daliban makaranta. A cikin sanarwar da mataimakiyar ministar ta musamman kan harkokin sadarwa, Nneka Ikem Anizebe ta fitar, ta bayyana cewa, akwai banbanci tsakanin shirin ciyar da daliban makarantun sakandaren gwamnatin tarayya da shirin ciyar da yaran makaranta da ake kira “Home Grown School Feeding” da ake aiwatarwa a wadansu makarantun firamaren kasar.

A wani taron bayyana halin da ake ciki kan annobar CODVID-19, wanda kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar ke kira a watan Agusta, Minista Sadiya Farouq ta sanar da cewa, sun kashe Naira miliyan 523.3 wajen ciyar da yaran makaranta da abinci a jihohi uku a lokacin kulle. Ministar ta bayyana cewa, an yi wa tsarin kwaskwarima domin iya gudanar da shi kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta. Ta kuma bayyana cewa an aiwatar da shirin ne bayan zaman tuntuba da gwamnonin jihohin.

Tun farko shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin neman hanyar ci gaba da ciyar da yaran makarantar a lokacin kulle wadanda ya ce da dama hanyar samun abincin da ya dace ke nan kasancewa galibi ‘ya’yan talakawa ne.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG