Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Baiwa 'Yan Kwangila Mako Biyu Su Kammala Aikin Gyaran Gadar-Tatabu.


Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo.

Mukaddashin shugaban Najeriya Parfessa Osinbanjo ne ya bada wa'adin lokacinda ya kai ziyara inda gadar ta rufta a jhar Nija.

A Najeriya, gwamnatin kasar ta baiwa ‘yan kwangila wa’adin mako biyu su kammala aikin gyaran gadar Tatabu dake jahar Nija, wacce ta hada arewa maso yammacin kasar da kuma kudancinta.

Mukaddashin shugaban Najeriyan parfessa Yemi Osibanjo, ne ya bada wannan wa’adi ranar Litinin, lokacin da ya kai ziyarar ganema idanuwansa inda gadar ta Tatabu ta rufta makonni da suka wuce, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi.

Parfessa Osinbajo, wanda Gwamnan Jahar Abubakar Sani Bello ya raka, yace gwamnatin tarayya zata kashe sama da Naira Miliyan dubu biyu domin wannan aiki, saboda muhimmancin gadar da hanyar kanta wajen zirga zirga ta kasuwnci tsakanin sassan kasar.

Da yake magana, Gwamna Sani Bello, ya gayawa Mr. Osinbanjo cewa, daya daga cikin hanyoyin da za’a bi na inganta hanyoyin, sun hada harda sa ido kan irin yawan kayayyaki da motocin dakon kaya suke dauka.

Daya daga cikin shugabannin kungiyoyi matuka motocin kasuwa, wanda ya zanta da wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari, ya yaba da wannan kwangilar. Daga nan ya bayyana fatar cewa masu aikin kwangilar zasu kammala aikin kan wa’adin da aka tsayar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG