Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wacce Kungiya Ce Za Ta Lashe Kofin Premier, Man City Ko Liverpool?


Karawar Liverpool da Man City a gasar FA
Karawar Liverpool da Man City a gasar FA

A ranar Lahadi, Man City za ta kara da Aston Villa yayin da Liverpool za ta fafata da Wolves.

Kungiyoyin Manchester City da Liverpool na haroro kofin gasar Premier League yayin da suke saman teburin gasar da tazarar maki daya tal.

City na saman teburin da maki 90 yayin da The Reds take da maki 89.

Liverpool ta farfado da burinta na lashe kofin gasar bayan da ta lallasa Southampton da ci 2-1 a wasan da suka buga a ranar Talata.

Yanzu wasanni biyu ne za su fayyace kungiyar da za ta lashe wannan Kofi.

A ranar Lahadi, Man City za ta kara da Aston Villa yayin da Liverpool za ta fafata da Wolves.

Wadannan wasannin da za a buga a ranar Lahadi 22 ga watan Mayu, musamman tsakanin Man City da Aston Villa su ne za su nuna wanda zai daga kofin.

Ga Yadda Lissafin Yake:

  • Idan Man City ta lashe wasanta da Aston Villa, ya zama ta lashe kofin Premier.

  • Idan Man City ta tashi da kunnen doki ko ta sha kaye a hannun Aston Villa, Liverpool kuma ta ci wasanta da Wolves, ya zama Liverpool ce za ta lashe kofin

  • Idan City ta yi kunnen doki da Aston Villa, Ita ma Liverpool ta yi kunnen doki da Wolves, ya zama City ce ta lashe kofin

Duk da wannan lissafi, masu sharhi dai a fagen kwallon kafa na ganin, komai yana hannun Man City a wannan lalen.

Idan kuma ta lashe wasanta da Villa, ya zama ta lashe kofin na Premier sau hudu cikin shekara biyar.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG