Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda Su Ka Mutu A Harin Afghanistan Na Baya Bayan Nan Yanzu Sun Kai 100


Wasu na kokarin taimaka ma wani da ya ji rauni a inda aka kai harin..
Wasu na kokarin taimaka ma wani da ya ji rauni a inda aka kai harin..

'Yan kwanaki bayan wani harin kunar bakin waken da aka kai wani babban otal a Kabul, babban birnin Afghanistan, sai kuma gashi an sake kai wani mummunan harin kuma har mutane wajen 100 sun halaka.

Yau dinnan Asabar wani harin kunar bakin waken da aka kai ta mota ya barraka wani wuri mai cinkushe da jama’a da ke wajen wani ginin gwamnati a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan ya kashe mutane akalla 95 baya ga wasu 163 da su ka ji raunuka.

Ma’aikatar Lafiyar kasar ce ta tabbatar da wannan adadin.

An hango turnukakken kura da hauhawar bakin hayaki na tashi sama a yankin tsakiyar babban birnin kasar bayan aukuwar fashewar a daura da ginin tsohuwar Ma’aikatar Cikin Gidan Afghanistan, a cewar shaidu.

Wani mai magana da yawun Ma’aikatar Cikin Gidan Afghnistan mai suna Nasrat Rahimi, ya ce maharin ya yi amfani ne da wata motar daukar majinyata, wadda ya loda wa bama-bamai, wajen kai harin a inda wasu fararen hula su ka taru sosai.

Tuni kungiyar Taliban ta bugi girji ta ce ita ta kai harin. Wani mai magana da yawun kungiyar ‘yan bindigar ya ce an yi niyyar auna wata babbar tawaga ce ta sojojin Afghanistan.

Amurka ta yi Allah wadai da wannan harin, wanda ta bayyana da na rashin kan gado.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG