Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadanda Su ka Mutu A Ivory Coast Sun Kai 462 Inji Wani Jami'in Majalisar Dinkin Duniya

Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS kenan bayan taronsu na Abuja, inda su ka tattauna matsalar Ivory Coast da sauransu
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS kenan bayan taronsu na Abuja, inda su ka tattauna matsalar Ivory Coast da sauransu

Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast ya ce dakarun da ke biyayya ga shugaban Ivory Coast da ke kan gado Laurent Gbagbo, na ta harbe-harben kai mai uwa da wabi kan wuraren da su ke jin masu goyon bayan Alassane Ouattara ne.

Jami’in rajin kare ‘yancin dan adam Guillaume Ngefa ya fadi a wani taron manema labarai a yau Alhamis cewa wannan harbe-harben da sauran hare-haren sun hallaka a kalla mutane 50 a makon jiya, ciki hard a yara 5 bayan dinbin wadanda su ka sami raunuka.

Ngefa wanda ke magana daga birnin Abidjan, y ace hare-haren sun sa adadin wadanda su ka mutu tun farkon rikicin day a biyo bayan zaben ya kai mutane 462.

Gbagbo dai ya yi biris da kiraye-kirayen Majalisar Dinkin Duniya, da Tarayyar Afirka, da kuma wani bangare na Afirka wato ECOWAS cewa ya mika ragamar iko. Dukkannin wadannan hukumomi ukun sun ayyana Mr. Ouattara a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba.

XS
SM
MD
LG