Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WAEC Ta Rike Sakamakon Zamfara


FILE

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da Hukumar Jarrabawa ta WAEC ta rike sakamakon jarrabawar dalibai saboda kasa biyan kudin daukar jarrabawa. Hukumar ta bayyana cewa tana bin jihohi 13 kudade.

To dama idan ana lura, jihohin arewacin Najeriya na daga cikin wadanda suka ci baya a neman ilimin zamani. Sashen Hausa ya tattauna da mataimakin gwamnan Jihar Mallam Ibrahim Wakkal.

“Wato inda matsalolin suke na farko mun binciko wasu, sai muka ga abinda ke gare mu, muna ta kokari mu biya bashin farko, sannan sai muka dawo muna cika na baya. To muna tattaunawa da hukumar WAEC” a cewar Mallam Wakkal.

“Bana a duk Najeriya an samu matsala ta kudi kowa ya san wannan, saboda haka sai ya kasance sun rike sakamakon jihohi da dama”.

Ko ina ilimin zamani ya nufa a jihar Zamfara?

Mataimakin gwamnan yace “abuda zan iya cewa shine Jihar Zamfara kamar wasu Jihohin arewa akwai cibaya kwarai da gaske a bangaren ilimi na zamani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG