Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilin MDD dake Kula da Matsalolin 'Yan Gudun Hijira Ya Ziyarci Jihar Borno


Mark Lowcock, en tournée dans le bassin du lac Tchad, au Niger, le 10 septembre 2017. (VOA/Abdoul-Razak Idrissa)
Mark Lowcock, en tournée dans le bassin du lac Tchad, au Niger, le 10 septembre 2017. (VOA/Abdoul-Razak Idrissa)

Makon jiya ne wakilin Majalisar Dinkin Duniya kuma mataimakin babban sakataren majalisar Mr. Lowcock mai kula da ayyukan agajin gaggawa ya kai ziyarar gani da ido jihar Borno inda ya sha alwashin gabatar da matsalolin 'yan gudn hijira gaban taron kolin majalisar da zai wakana makon gobe

A makon nan ne sabon mataimakin sakataren majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan jin kai da bada agajin gaggawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya Mr Mark Lowcock ya kai ziyarar aiki ta yini biyu sansanonin ‘yan gudun hijira a yankin da kuma wasu sassa na Jamhuriyar Nijar.

Masu fashin baki da kungiyoyin rajin ‘yancin ‘yan gudun hijira a Najeriya sun fara bayyana hasashen dangane da sakamakon da ziyarar zata haifar.

Mr Mark Lowcock ya ziyarci garuruwan Gwoza da Pulka a jihar Borno, inda ya yi tozali da wasu daga cikin daruruwan mutane yara da mata da kuma tsoffin dake cikin talauci da yunwa da rashin muhalli sanadiyyar tarzomar Boko Haram.

Mr Lowcock wanda ya fara aiki a ranar daya ga wannan wata na Satumba, ya sha alwashin gabatar da bukatar kara kaimi ga shugabannin duniya da hukumomi wajen tallafawa wadannan mutane a yayin taron koli na Majalisar Dinkin Duniya, MDD, da zai wakana a makon gobe.

Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero masani ne kan sha’anin hukumomin kasashen duniya da lamuran diplomasiyya ya bayyana dalilan da suka sa wasu kasashe na marmarin tallafawa wadanda suke cikin matsala a kasashensu.

To amma comrade Kabiru Sa’idu Dakata na gamayyar kungiyoyin fararen hula masu rajin kiyaye hakkin ‘yan gudun hijira a yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa yawancin tallafin da kasashen duniya ke bayarwa basa isa wadanda suke bukata saboda barayin dake karkatasu wasu wuraren. Idan kuma kudi aka bayar barayin biro sais u sace. Ya kira gwamnati ta dauki matakan hukumta duk masu zarmiya da taimakon da duniya ke bayarwa.

A halin da ake ciki ana sa rai dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai halarci taron kolin na Majalisar Dinkin Dunniya, MDD, wanda zai gudana a birnin New York a Amurkamako mai zuwa kuma batun neman tallafi game da yaki da mayakan Boko Haram zai zama jigon jawabin da zai gabatar a zauren taron.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG