Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wane Ne Sabon Kocin Chelsea Thomas Tuchel?


Sabon Kocin Chelsea, Thomas Tuchel
Sabon Kocin Chelsea, Thomas Tuchel

Kwanan nan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke wasa a gasar Premier ta Ingila ta sanar da Thomas Tuchel a matsayin sabon kocin club din.

Hakan na zuwa ne bayan da ta sallami Frank Lampard a farkon makon nan.

Thomas Tuchel, mutum ne da ya yi sabgogi da dama a rayuwarsa, a da, shahararre ne fannin kwallon kafa, amma raunin da ya taba ji ya sa ya ajiye kwallon kafa a gefe.

Tuchel dan asalin kasar Jamus ne, ya taba bugawa Augsburg, Stuttgarter Kickers da SSV Ulm wasa.

Amma raunin da ya ji a lokacin yana ganiyar fara tashe, wato yana dan shekara 24 ya sa ala tilas ya daina kwallo.

An haife shi ne a ranar 29 ga watan Agustan 1973 a yammacin kasar Jamus. Ya kware a fannin harshen Ingilishi.

Ya taba horar da Borussia Dortmund ta kasar Jamus da kuma PSG ta kasar Faransa.

Thomas Tuchel, lokacin yana horar da PSG
Thomas Tuchel, lokacin yana horar da PSG

Wani sharhi da shafin gidan talbijin na Fox Sports ya yi, ya ruwaito cewa Tuchel ya taba harkar tallata kayan zamani, wato model a harshen Ingilishi.

Ya kuma taba aiki a matsayin mai sayar da barasa, sannan ya karanci fannin ilimin tattalin arziki.

Nada shi a matsayin kocin Chelsea na zuwa ne bayan da kungiyar PSG ta sallame shi a ranar jajiberin Kirsimeti, watannin bayan da ya kai kungiyar wasan karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

A shekarar 2016, ya taba neman aikin horar da ‘yan wasan Chelsea, amma aka ba Antonio Conte aka ki daukan shi.

Yanzu Chelsea ta dauke shi akan kwantiragin wata 18 tare da yiwuwar tsawaitawa idan al’amura sun daidaita.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG