Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Ba' Amirke Bakar Fata ya Harbe 'Yan Sanda a New York


Shugaban Amurka Barack Obama yayi Allah wadai da harbe wasu 'yan sanda biyu da suke aiki da birnin New York har lahaira.

Shugaban Amurka Barack Obama yayi Allah wadai da harbe wasu 'yan sanda biyu da suke aiki da birnin New York har lahaira, da rana tsaka yayinda suke zaune a cikin motar su ta aiki.

Shugaban wanda yake hutu a Hawa'ii, yace ba kamar sauran jama'a ba, barade biyu ba zasu sami damar komawa ga iyalansu ba. Mr. Obama yace kuma babu hujjar kashe su.

Fadar White House tace shugaba Obama ya kira kwamishinan 'Yansanda na binrin New York William Bratton, yayi masa ta'aziyya.

Shugaban na Amurka ya sake nanata kiransa ga Amurkawa suyi watsi da tarzoma, maimakon haka suyi amfani da abunda ya kona musu rai wajen wanzarda zaman lafiya.

'Yansandan biyu suna zaune ne a cikin mota a unguwar Brooklyn, lokacinda maharin dan shekaru 28 da haifuwa Ismayyil Brinsley ya taho kansu ya bude musu wuta kai tsaye. Daga bisani ya gudu zuwa cikin wata tashar jiragen kasa inda ya harbe kansa.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG