Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bincike Ya Nuna Mutane Kalilan Ne Suka Yada Cutar Ebola A Yammacin Afirka


Ma'aikatan Kiwon Lafiya da suka yi yaki da cutar Ebola
Ma'aikatan Kiwon Lafiya da suka yi yaki da cutar Ebola

Wani sabon bincike ya tabbatar da cewa kalilan cikin wadanda suka kamu d a cutar Ebola, sune suka yada cutar a yammacin Afirka.

Masu bincike a jami'ar Princeton dake New Jersey, da kuma jami'ar jahar Oregon anan Amurka suka gudanar, sun gano cewa kashi uku cikin dari na wadanda suka kamu da cutar sune sarsalar kashi 61 cikin dari na wadanda suka kamu da cutar.

An wallafa sakamakon binciken ne cikin wata mujallar kimiyya da ake kira Proceedings of the National Academy of Sciences.

Kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fada, an sami fiyeda mutane dubu 28 wadanda suka kamu da cuutar tsakanin watan oktoba shekara ta 2014 zuwa watan Maris 2015, da suka haddasa mutuwar fiye da mutane dubu 11.

XS
SM
MD
LG