Accessibility links

Wani Bom ya Fashe a Gidan Cinema Dake Maiduguri


Wasu gidaje da aka kona a harin da ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kaishi a Kawuri dake Maiduguri, Junairu 28, 2014

Misalin karfe shida na maraicen Najeriya ne Asabar dinnan, wani Bom ya fashe a wani gidan cinema dake anguwar Ajilari binta suga a birnin Maiduguri.

Wannan cinema dai kamar kasuwa take, inda akwai masu hada-hadar kasuwanci da saye da sayarwa, sannan waje ni inda jama’a suke kallon wasannin kwallon turai.

A yammacin yau dinne a lokacin da jama’a ke kallon wasan kwallo, wani bom ya fashe a cikin cinema din. Jama’a sun taru suna aikin kwashe wadanda abunda ya rutsa dasu, wani bom na biyu ya kara tashi, kuma ya kashe mutane da yawa.

Shaidun gani da ido, sunce da yawa daga cikin wadanda harin ya shafa yara ne da mata, yawancinsu ‘yan talla da kananan kasuwanci.

Kawo yanzu dai ba’a san adadin mutanen da wannan tashin hankali ya kashe ba, amma jami’ai sun killace wajen.

Mutanen wannan unguwa sun fara ficewa saboda tsoron ko maharan sun zagaye wannan unguwa ne.

Birnin Maiduguri ya sami kanshi a cikin wani hali, tun bayanda mayakan sa kai na Boko Haram suka fara tayar da kayar baya a shekara ta 2009.

XS
SM
MD
LG