WASHINGTON, D.C —
Wani dan bindiga a birnin Milwaukee jihar Wisconsin da ke nan Amurka, ya kashe mutane 5 kafin ya kashe kansa a jiya Laraba, a wani kamfanin sarrafa barasa da ake kira Molson Coors.
“Yan sanda sun ce dan bindigar namiji ne dan shekaru 51 da haihuwa, amma basu bayyana sunansa ba da kuma sunayen mutanen da ya kashe, har sai an sanar da iyalan su.
A jiya Laraba, Shugaba Donald Trump ya soma jawabin bude wani taron manema labarai a fadar White House game da cutar Coronavirus, da bayyana harbin a matsayin “Mummunan al’amari”. Ya kuma jajantawa al’ummar Wisconsin da kuma iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Ya zuwa yanzu dai ‘yan sanda ba su bada wani cikakken bayani a kan harin ba ko dalilin da ya sa dan bindigar ya kai harin.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama
-
Fabrairu 22, 2021
COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka
-
Fabrairu 20, 2021
Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance
-
Fabrairu 17, 2021
Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka
Facebook Forum