Accessibility links

Wani Dan Boko Haram Ya Tabbatar Da Mutuwar Shekau


Imam Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko-Haram.

Wani dan kungiyar Boko Haram da aka cafke ya tabbatar da mutuwar Shaikh Abubakar Shekau a wani gumurzu da kungiyar ta yi da sojojin Najeriya

Makon da ya wuce ne dakarun sojojin Najeriya suka sanar cewa shugaban kungiyar Boko Haram ya rasu a wani asibiti a garin Amidtche cikin kasar Kamaru sanadiyar raunin da ya samu lokacin da kungiyar ta fafata da sojoji a wani hari da aka kai mata.

Sanarwar ta sojojin Najeriya ta jawo cece-kuce domin rashin tabbacin lamarin . To amma hoton wani saurayi da 'yan mayakan sa kai da aka sani da 'Yan Gora suka fitar sun ce mutumin ya tabbatar masu da mutuwar Shekau. Kamar yadda suka fada saurayin ya ce Shekau ya gamu da ajalinsa ne a wani gumurzu da aka yi a garin Marte sabili da mugun raunin da ya samu har ya kai ga mutuwarsa. Wannan abun da saurayin ya fada ya sabama abun da sojoji suka fada. Su, sun ce Shekau ya samu rauni ne a fafatarwarsu a dajin sambisa daga bisani ya samu ya tsere zuwa wani asibiti cikin kasar Kamaru.

Da yake amsa tambayoyi saurayin ya ce Shekau ya mutu a Marte. Ya ce ya samu rauni ne tun lokacin da aka kai hari a dajin sambisa. Wannan furucin ya zo daidai da na sojoji. Amma yaron ya ce lallai a Marte Shekau ya mutu kuma shi kansa ya ga lokacin da aka binne shi. Yaron da ya hakikance cewa Shekau ya mutu ya ce shi bai taba kashe mutum ba sai dai akan bashi bindiga ne kawai ya rike idan an kashe mutum akan bashi nera dubu biyu zuwa dubu uku. Ya ce yana kan koyon yadda ake harbi da bindiga.

Matasan dake zakulo 'yan Boko Haram da ake kira fararen hulan JTF ko 'Yan Gora na cigaba da kwakulo 'yan kungiyar da tsaro a duk fadin Maiduguri da kewaye. Suna binciken duk wadanda zasu fita ko su shiga Maiduguri. Duk da wani zibin matasan sukan rasa rayukansu amma basu karaya ba sai ma karin matasa suke yi har ma da mata.

Ga Haruna Dauda Biu da karin bayani.

XS
SM
MD
LG