Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kasuwa a Kaduna Ya Kalubali Shugabannin Addinin Musulunci Akan Tsaro


Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau

Shahararrun malaman addinin Musulunci da attajirai musulmai su ne suke da gagarumin gudunmawar da zasu bayar kuma a sauraresu.

Dan kasuwan yace a matsayinsa na dan kasuwa yana da jama'a daga koina a kasar da yake muamala dasu.

Sau da yawa idan yana zantawa dasu suna ganin addinin Musulunci addini ne da yake karantar da hargitsi da kashe-kashe. Yace ba haka ba ne. Akwai ayoyi da yawa a Kur'ani da suka ce kashe mutum ba tare da shari'a ba nada hukunci.

Rashin wayar da kawunan mutane ya jawowa addinin Musulunci gagarumin gyamarsa ga wanda bai san addinin ba. Yace amma yau malaman musulunci da atttajiran addinin su ne Allah zai fara tambaya domin basu bada cikakken gudunmawa wanda zai taimakawa wanda baya addinin ya san yadda addinin yake karantarwa. Yace shin mutum nada ayar da aka ce ya fadawa wanda baya addinin Musulunci ya kasheshi. Yace sai idan sun tsokaneka ne zaka rama kamar yadda Allah yace.

Yayi misali da Sardauna Sir Ahmadu Bello wanda ma'ajinsa kirista ne haka kuma mataimakinsa na kusa dashi kirista ne. Amma yau an raba kawunan mutane. Yace babu dole a batun addini. Idan mutun ya ga dama ya bautawa wuta. Yace dabi'un mutum ne zasu sa wasu su yi sha'awar addininka amma ba tare da tarzoma ba.

Siyasa tayi tasiri akan abubuwa biyu wato shugabanci da kudi dalili ke nan suka yi anfani da addini. Ya kira su ji tsoron Allah domin akwai ranar gamuwa da Shi. Yace Musulmai sun taimakawa tabarbarewar tsaro kashi saba'in cikin dari. Yace yau sai gashi an wayi gari wasu sun dauki hukunci a hannunsu. Ana kallo ana ta yiwa addinin Allah batanci. Su wadanda ba Musulmai ba ne basu gane cewa abun dake faruwa ba addinin musulunci ba ne ba kuma karantarwar musulunci ba ne. Yace attajirai sun kasa fitar da kudi da malaman kwarai zasu iya koyaswa ta kafofi daban daban.

Akan mafita yace mu yadda Allah ne ya hadamu zama tare. Na biyu a koma ana ta yin tuba zuwa ga Allah domin an saba mashi. Na uku gwamnati ta mayar da hankali ta gane jama'ar kasa Musulmi da Kirista basa jin dadin rayuwa idan dai a arewacin kasar ne. Gwamnati ta taimaka da kuma taimako Allah za'a kawo karshen bala'in da ya addabi kasar.

Ga rahoton Lawal Isah Ikara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye


Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG