Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 35 A Syria


Shugaban Syria Bashar al-Assad
Shugaban Syria Bashar al-Assad

Fashewar da ta auku yau Jumma’a a wani wajen tsaron na ‘yan hamayya dake kauyen Sousian, ta kashe farin kaya da dama da kuma dakarun hamayya.

Mutane da dama sun taru a ofishin tsaron inda suke neman izinin komawa al-Baba da fadan da aka yi na tsawon watanni ya daidaita.

Dakarun kasar Turkiya da na ‘Yan tawaye sun shiga garin jiya alhamis bayan janyewar mayakan IS, abinda ya kawo karshen fada da ake yi da nufin kwace wurin dake karkashin ikon Is bisa ga cewar kafar watsa labaran kasar Turkiya da kuma kungiyoyin ‘yan gwaggwarmaya na Syria.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG