Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Alhamis Wakilin MDD Ya Gana da Tawagar Gwamnatin Siriya A Geneva


 STEFFAN DE MISTURA, wakilin MDD na musamman a Syria
STEFFAN DE MISTURA, wakilin MDD na musamman a Syria

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ko MDD Steffan de Mistura na musamman a Syria ya gana da tawagar gwamnatin Syria a yau Alhamis a birnin Geneva yayinda yake kaddamar da sabon shirin kawo karshen yakin basasan kasar wanda aka kwashi shekaru shida ana gwabzawa tsakanin dakarun gwamnati da wasu kungiyoyin ‘yan tawaye.

Akwai kuma shirin ganawa da Steffan de Mistura zai yi da wakilan jami’iyar adawa a yau Alhamis, wuni guda bayan yace bai ga wata alama da nuna za’a cimma nasarar warware rikicin ba, amma sai yanayin siyasa na wannan lokaci na nuna yuwuwar samun zaman lafiya.

Bangarori masu yaki da juna na Syria sun gana da juna a birnin Geneva kimanin watanni tara a can baya. Tattaunawarsu ta sake warware dalilin sake barkewar rikici bayan yarjejeniyar tsagaita wuta.

De Mistura ya amince cewar nasarar sake komawa ga tattaunawa da bata yi tasiri a baya ba, zata ta’allaka ne ga hada kan bangarorin wurin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wutar ta yanzu.

Yace Rasha da ta tsara yarjejeniyar tare da Turkiya a Astana babban birnin Kazakhstan, tana amfani da karfin fada nata wurin ganin an yi aiki da shirin tsagaita wuta.

De Mistura ya kara da cewar ya yi kira ga sauran kasashe da suke fada ‘yan adawar su ji, da su gargadesu su yi aiki da shirin tsagaita wutar kuma su daina takalar waccan bangare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG