Paris ya zamo wata babban birnin dake cikin wani sabon hadari domin yana makokin tabioin ‘yan taadda.
Wani da aka haifa a Chechen, amma ya zama Bafaranshe ya tinkari mutane da wuka, inda ya kashe mutun guda kana ya jima 4 rauni. Dama dai wannan dan taliki yana cikin jerin ‘yan ta’adan da aka sawa ido, to sai dai kokarin sa na kai hari a ranar Asabar ya nuna a sarari irin babban kalubalen tsaron da kasar ta Faransa ke huskanta game da ‘yan ta’adda, inji jamiian Faransan.
Yanzu haka dai mutane sama a 2,600 ne da ake tuhumar ‘yan ta’adda ne da suke cikin jerin mutanen da ake sawa ido, to sai dai kuma ba za a iya samun zarafin sa musu ido gaba dayan su ba.
Wani masani harkokin ta’addanci Olivier Guita yace wannan shine karo na 12 da mahara suka yi nasarar kai hari Faransa, tun daga shekarar 2013, kuma wannan na kwanan nan shine hari na biyu da yan ta’addan suka yi nasara a ciki wannan shekarar.
Facebook Forum