Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Harin Bazata Da Aka Kai A Syria Ya Hallaka Mutane 27


A kalla dakarun Syria 27 ne aka kashe, wasu uku kuma suka jikkata a wasu hare-hare biyu da mayakan da ke da alaka da kungiyar al-Qaida suka kai jiya Alhamis, a tsakiyar lardin Hama na kasar Syria.

Hare-haren biyu na bazata an kaisu ne kan sojojin Syria, a kusa da kauyen Atshan da ke arewacin yankin Hama al-Bayaan, shafin yanar gizo ne da ke zama hanyar yada labaran ‘yan ta’adda a Syria.

Sai dai shafin al-bayaan har ila yau ya wallafa wata sanarwa daga kungiyar, na cewa ta kaddamar da hare-hare kan dakarun gwamnatin Syria a wasu yankunan Hama da kuma arewa maso yammacin lardin Idlib.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG