Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Sama Da Mutane 40 A Arewacin Siriya


An hallaka mutane fiye da 40 sannan wasu da dama sun samu raunuka a birnin Qamishli na arewacin Siriya, a wani harin kunar bakin waken da aka kai da motar daukar, wanda kungiyar ISIS ta yi ikirarin kaiwa.

Wakilin Sashen Kurdanci na Muryar Amurka Zana Omar, na daya daga cikin wadanda su ka samu raunuka a harin, wanda aka kai daura da kan iyakar Turkiyya. "Harin na bam ya auku ne da nisar kimanin mita 50 daga gidan da na ke," abin da ya gaya ma Muryar Amurka kenan, Ya kara da cewa, "Mata ta da 'ya'yenmu biyu sun samu raunuka a harin. Gida na ya lalace kwatakwata."

Ya kuma ce wasu daga cikin 'yan'uwansa da ke unguwar sun bace bayan harin bam din; ya ce "mai yiwuwa su na binne karkashin baraguzai."

Rami Abdel Rahman na kungiyar kare hakkin dan adam a Siriya mai hedikwata a Burtaniya ya gaya ma gidajen labaran Larabawa cewa harin bam din ya ruguza bangaren hedikwatar dakarun Kurdawa da ke iko da Yammacin Qamishli. Gwamnatin Siriya ce ke iko da wani babban bangare na birnin, ciki har da wani babban filin jirgin sama na yaki.

ISIS ta dau alhakin kai harin ne a wani bayanin da aka buga a shafin kamfanin yada labaranta da ke yanar internet, inda ta ce ta auna dakarun kurdawa ne.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG