Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jami'in Majalisar Dinkin Duniya Ya La’anci Wulakancin Da Ake Yi Wa Ma’aikatan Bada Agaji A Sudan Ta Kudu


Wani babbar kusar Majalisar Dinkin Duniya ya la’anci wulakancin da yace ana yi wa ma’aikatan bada agaji na kasa da kasa dake aiki a kasar Sudan ta Kudu, wanda yace hakan na hana a iya kai agaji ga kusan mutane milyan bakwai masu bukatar agajin.

Mark Lowcock, wanda shine karamin sakataren hukumar kula da ayyukkan bada agaji na majalisar, yace a cikin wattani biyu kacal da suka gabata, ma’aikatan bada agaji guda hudu aka hallaka, aka kuma sace wasu kamar 10 a kasar.

Sai dai ga dukan alamu, kiddidigar tashi bata hada da wasu ma’aikatan bada agaji da aka yi awon gaba da su a garin Yangiri na gabashin kasar ba.

Lowcock, wanda ya ziyarci Sudan ta Kudu a cikin wannan makon, yace da gwamnatin kasar da kungiyoyin ‘yan adawa ba wanda ya dauki wani mataki na ja wa mutanensa burki wajen hana su toshe hanyoyin hana ma’aikatan bada agaji kaiwa inda suka tasar wa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG