Accessibility links

wasu sun nuna rashin amincewar su akan kasancewar sojojin Faransa da na Amurka a janhuriyar Niger

An sami rahoton cewa wani jirgin saman kasar Farasan mai tuka kansa, da ke aikin tsaro a Bataliyar Barkan ya fadi a tashar saukar jiragen kasa-da-kasa na Diori Hamani dake birnin Yamai, wajen karfe 3 na daren jiya.

Rahotanni sun ce duk da cewa babu hasarar rayuka sakamakon faduwar jirgin, faduwar ta haddasa lalacewar hanyoyin jirgin sama wanda hakan ya tilasta ma jami’an jirgin hana tashi da kuma saukar wasu manya-manyan jirage a filin saukar jiragen saman. Hakan kuma ya haddasa karkata wasu jiragen saman da ke jigilar mahajjata zuwa birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso da kuma jihar Kano a kasar Najeriya.

Malam Mustapha kadi Ummani jami’in kula da jiragen sama, ya tabbabatar ma wakilin murya Amurka, Abdullahi Mamman Ahmadou cewa tashar jirgin na nan rufe ga manyan jirage.

Faduwar jirgin saman ya kara maido da batun kasancewar sojojin Faransa da na Amurka a janhuriyar Nijer. Da kuma hadarin da ke tattare da irin shawagin da jirigin mara matuki ke yi ga fararen hula.

Malam Nuhu Mahammadu Arzika ya bayyana fargabansa akan irin wadannan jiragen, yace ba a san inda hadarin zai kara awkuwa ba, kuma a cewar shi bai ga wani alheri tattare da kasancewar wadannan sojojin ba a kasar.

A shekarar 2013 ne gwamnatin kasar Nijer ta ba kasashen lamunin samun wani sansanin soja domin gwagwarmayar kwato kasar Mali daga hannun ‘yan ta’adda.

XS
SM
MD
LG