Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani 'Karamin Yaro Ne Ya Kai Harin Kunar Bakin Wake A Turkiyya


Gawar wani da aka kashe sakamakon harin kunar bakin wake a Turkiyya

Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayip Erdogan, yace harin kunar bakin waken da wani saurayi ya kai a wajen wani bikin aure a Kudu maso Yammacin kasar ya hallaka mutane 51 kana wasu da dama sun samu mummunar rauni.

Erdogan yana magana a ranar asabar, yace bayanan farko sun nuna cewa 'dan harin kunar bakin waken bai wuce tsakanin shekaru 12 zuwa 14 ba.

Yace ga bisa dukkan alamu kungiyar IS ce ta kai wannan harin a birnin Gaziantep, dake kusa da bakin iyakar Syria.

A cikin jawabin Erdogan na farko, yace kungiyar IS bata da banbanci da ta Kurdawan nan na PKK, da kuma mabiya Shehin malamin nan dake zaune nan Amurka Fetullah Gulen, wanda shugaba Erdogan yace yana da hannu dumu-dumu wajen yunkurin yi masa juyin mulki. A cikin watan da ya gabata.

A cikin sakon Erdogan yace abin da muke son mu fada wa masu kai mana hari shine ba za suyi nasara ba.

Fadar White House tayi Allah wadai da wannan harin da aka kai a birnin Gaziantep, tace masu wannan mummunar 'dabi'a su rasa inda zasu kai hari kuma sai wurin bikin aure.

A cikin sanarwar da aka fitar daga fadar ta White House tace mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, zai ziyarci kasar ta Turkiyya domin jaddada wa kasar aniyar Amurka ta aiki tare domin yaki da ta'addan ci.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG