Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hoton Bidiyon Yaron Syria Ya Ja Hankula a Duniya


Wani faifan bidiyo da ya nuna wani karamin yaro a Syria jina-jina bayan hare-haren da jiragen sama su ka kai a Aleppo, ya ja hankula jama'a a duniya. Hoton dai ya karade shafukan sada zumunta musamman a kafar Youtube.

Hoton ya nuna yaron zaune a galabaice a cikin motar daukar marasa lafiya kuma fuskarsa ta turnuke da jini da kuma kura.

Wani likita Aleppo mai suna Osama Abu al-Ezz ya gano yaron dan shekaru biyar ne kuma sunansa Omran Dagneesh.

Ya tabbatar da cewa an kai yaron ne a wani asibiti da ake kira M10 a yammacin Laraba kuma an masa jinyar rauni da ya samu a ka har an sallame shi.

Yaron ya samu raunin ne biyo bayan wani hari ta sama da aka kai a wata unguwar da 'yan tawayen su ke ta Qaterij.

Wani likita a asibitin M10 ya ce mutane takwas ne suka mutu a wannan harin ciki har da kananan yara biyar.

XS
SM
MD
LG