Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kamfanin Najeriya Zai Baiwa Manoman Nijar Kayan Noma Na Zamani


Traktoci na noman zamani

Inji Alhaji Garba Bawa manoman Nijar sun bukaci kamfaninsu ya basu traktocin noma tare da takin zamani a karkashin wata yarjejeniyar da gwamnatn kasar zata marawa baya.

Manoman na kasar Nijar sun hada kai a kungiyance suna neman kamfanin Najeriya ya basu kayan noma na zamani tare da taki domin inganta samun cimaka a kasar.

Bukatar manoman Nijar ta biyo bayan irin hadin kan da kungiyar manoma shinkafa a Najeriya suka yi inda kamfanin na Alhaji Garba Bawa ya basu kayan aiki bisa ga wata yarjejeniya.

Kayan da kamfanin zai ba manoman kudinsu ya dara nera biliyan dari takwas amma su manoman zasu biya kashi 25 cikin 100. Sauran kashi 75 kamfaninsa zata biya amma gwamnatin Nijar zata yi alkawarin biyan kudin cikin shekaru ukku. Alhaji Garba yace irin tsarin da ya kawowa Nijar ke nan.

Kafin a kawo kayan gwamnati zata bada kashi 30 cikin kudin. Shi kuma manomin da za'a tallafawa zai bada kashi 10. Sauran kashi 60 bayan da kamfanin ya samu kashi arba'in manomi kuma sai ya dinga biya kadan kadan. To saidai gwamnatin Nijar zata bada tabbacin biyan sauran kudin a rubuce. Zata biya cikin shekaru ukku.

Alhaji Garba Bawa yace ya gayawa Firayim Ministan kasar Nijar Birji Rafini cewa kamfaninsa zai saka jarin dalar Amurka dari biyu da hamsin a kasar a sabuwar shekarar nan mai zuwa. Zai dinga saka jarin $250m kowace shekara har na tsawon shekaru hudu, wato jimillar dala biliyan daya ke nan a jari kawai..

Inji Alhaji Garba Bawa Firayim Ministan Nijar yayi alkawarin bada tabbacin biyan kudin kayan aikin gonan nera biliyan dari hudu.

Bayan shekara daya, wato daga shekarar 2018 kamfanin Alhaji Garba Bawa zai kafa ma'aikatar sarafa taki a kasar Nijar din wanda zai kaiga kasashen dake makwaftaka da Nijar samun taki a saukake.

Wannan zai kawowa kasar Nijar alfanu da dama. Za'a samu aikin yi kana abinci zai wadatu.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG