Dakarun gamayyar rundunar MNJTF, bisa ga sanarwar da su ka bayar, sun yi wata arangama ne a wani sansanin mayakan na Boko Haram da ake kira Andakar a karshen makon da ya gabata, inda rundunar ta samu nasarar kashe kwamandan Boko Haram wanda ake kira, Malam Musa tare da wasu mayakansa 15.
Sanarwar ta kara da cewa an lalata wasu motocin kungiyar ta Boko Haram guda biyar, sannan an kama wata mata gyatuma, wacce ba a tantance alakarta da mayakan na Boko Haram ba.
Shi dai kwamanda Musa, mutum ne mai ido daya, shi ne kuma ya ke kula da garuruwan da ke kudancin yankin na tafkin Chadi, wadanda su ka hada da Daban Masara , Kirta Wulgo da kuma Koleram.
A cewar sanarwar, Musa ya yi kaurin suna wajen yawan sa kudaden haraji ga manoman yankin da masu sana’ar kamun kifi ko masunta, da kuma makiyaya, domin samar wa kungiyar ta Boko Haram kudaden shiga da ta ke amfani da su wajen kai hare-hare.
Facebook Forum