Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kwamandan Buharin Daji Ya Ce Yana Fata Za a Samu Zaman Lafiya


Buhari Tsoho wanda aka fi sani da Buharin Daji lokacin bukin yin sulhu a Katsina

A cikin wata hira da Muryar Amurka, wani babban kwamandan Buharin Daji, Lawwali Abubakar, ya tabbatar da mutuwar dan ta'addar, ya kuma ce su na son ganin an kawo karshen kashe=kashen da ake yi a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya

A cewar wani kwamandan mayakan Buharin Daji rokonsu shi ne Allah Ya kawo musu zaman lafiya domin su da matansu da 'ya'yansu su samu ci gaba.

Lawwali Abubakar yace suna iya bada hadin kai a zauna lafiya a jihar tare da kara cewa kowa ya bada makamin da ya mallaka.

Ya ce yana cikin kwamandojin kungiyar Buharin Daji idan kumma an ce an yadda a gyara suna goyon bayan haka dari bisa dari, a gyara kowa ya zauna lafiya.

Muryar Amurka ta tambayi kwamandan tabbacin da yake dashi cewa a wannan karon za'a samu zaman lafiya idan aka yi la'akari da yarjejeniyar da aka yi da kungiyar can baya da bai yi tasiri ba. Maimakon zaman lafiya rayuka aka dinga asararsu.

Kwamandan ya bada dalilan da suka sa yarjejeniyar da aka cimma can baya bata yi tasiri ba. A cewarsa Buharin Daji ya tura iyalansa, wasu zuwa makaranta wasu kuma sun tafi Saudiya amma sai aka kamesu aka yankesu. Ya nemi duk hanyar da zai amsosu lamarin ya cutura. Daga nan lamarin ya tabarbare kowa ya ja daga. Wannan ne ya kai ga yake yake.

Sun ji dadin bayanin mataimakin gwamnan jihar, kuma sun yadda da abubuwan da ya fada cewa a zauna lafiya. Domin an kashe Buharin Daji ba tabbaci ba ne na samun zaman lafiya. A nemi hadin kai a zauna lafiya.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:46 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG