Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya Yayi Allah wadai da Koriya ta Arewa


Kim Jong Un, shugaban Koriya ta Arewa
Kim Jong Un, shugaban Koriya ta Arewa

Bisa ga shin Koriya ta Arewa ta kera makaman nukiliya masu linzami duk da jan kunnuwanta da a keyi, wani kwamitin Majaisar Dinkin Duniya yayi tur da kasar

Wani kwamitin Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah wadai da Korea ta Arewa, saboda shirinta na kera makaman nukiliya da na masu linzami, yayin da al’umar kasar ke fama da yunwa.

Kungiyar Tarayyar Turai hade da kasar Japan ne suka jagoranci gabatar da wannan kuduri a gaban kwamitin kare hakkin bil’adama.

An kuma amince da shi a mataki na bai-daya, sannan za a mika shi ga babban zauren Majalisar ta Dinkin Duniya.

Kwamitin ya yi tir da kasar ta Korea ta arewa, “saboda yadda take karkata kudadenta domin kera makamin nukiliya da na masu linzami nau’in ballistic, a maimakon maida hankali kan kyautata rayuwar al’umarta.”

Kwararru sun yi amannar cewa, kashi 70 cikin 100 na al’umar kasar ta Korea ta Arewa, ba su da wadataccen abinci.

Sai dai jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya, Ja Song Nam, ya ce gwamnatinsa “ta yi fatali da wannan matsaya da aka cimma” yana mai cewa, “wannan wani nau’in takalar fada ne ta fuskar soji da siyasa, sannan shiri ne da aka kitsa hade da kulle-kullen Amurka da sauran abokan hamayya.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG