Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Matashi Bafalasdine Ya Soki Mutane A Wata Kasuwar Yahudawa Jiya Alhamis


Motar safa din da matashin ya fara kaiwa hari jiya Alhamis

Wani matashi Bafalesdine ya soki mutane da wuta tare da bude musu wuta a wata kasuwar Isra’ila a jiya Alhamis, wannan kuma yayi sanadiyyar raunata mutane 6, kafinjama’a suci karfinsa.

‘Yansanda sun bayyana wannan matashin dan shekaru 18 da haifuwa cewa mazaunin birninNablus dake yammacin kogin Jordan ne.

‘Yansanda da kuma shedun gani da idosuka ce da farko ya bude wuta kan wata safa a tsakiyar birnin Petah Tikya, kana daga bisani kuma ya auka cikin shagon sayar da keken dinki.

Wannan yasa masu sayayya a shagon suka shiga jifar sa kafin daga baya suka kai shi kasa, kuma suka mika shi ga ‘yansandan da suka kira.

Sai dai an daba wa wani dan taliki karfen kunce kusa sannan aka lakadawa wani duka bisa kuskuren cewa shine Bafalasdinen.

Sai dai kusan dukkan wadanda suka samu rauni sakamakon wannan harin ba wanda yake huskantar barazanar mutuwa.

Mai Magana da yawun ‘yansanda ya bayyana cewa jamia’an tsaro sun dauki wannan aiki ne na ta’addanci.

An sami sassaucin kai hare hare da wuka cikin ‘yan watannin nan- wanda ada ya zame ruwan dare gama gari tsakanin Falesdinawa da Yahudawa, bayan da jita-jita ta bazu cewa Isra’ila tana shirin kwace masallacin al-Aqsa dake birnin Qudus, mai tasiri ga musulmi da kuma Yahudawa.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG